31 Suka tashi tun da sassafe suka rantse wa juna, Ishaku ya sallame su, suka tafi cikin salama.
32 Ya zama kuwa a wannan rana, barorin Ishaku suka zo suka faɗa masa zancen rijiyar da suka haƙa, suka ce masa, “Mun sami ruwa.”
33 Ya sa mata suna Sheba, domin haka har yau sunan birnin Biyer-sheba.
34 Sa'ad da Isuwa yake da shekara arba'in, ya auro Judit, 'yar Biyeri Bahitte, da Basemat 'yar Elon Bahitte,
35 suka baƙanta wa Ishaku da Rifkatu rai.