1 Lokacin da Ishaku ya tsufa, idanunsa kuma suka yi duhu har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa, ya ce masa, “Ɗana!”Sai ya amsa, “Ga ni nan.”
2 Ishaku ya ce, “Ga shi, na tsufa, ban san ranar rasuwata ba.
3 Yanzu fa, ka ɗauki makamanka, da kwarinka da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama,
4 ka shirya mini abinci mai daɗi irin wanda nake so, ka kawo mini in ci, don in sa maka albarka kafin in rasu.”