36 Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yakubu ba? Gama sau biyu ke nan yake yi mini ƙwace. Ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi kuma, yanzu ya ƙwace mini albarkata.” Sa'an nan ya ce, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”
37 Ishaku ya amsa wa Isuwa ya ce, “Ga shi, na shugabantar da shi a kanka da dukan 'yan'uwansa na ba shi su, su zama barorinsa, na ba shi hatsi da ruwan inabi. Me zan yi maka kuma, ya ɗana?”
38 Sai Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Har da ni ma ka sa mini albarka, babana.” Isuwa ya ta da murya ya yi kuka.
39 Sai Ishaku mahaifinsa ya amsa masa ya ce,“Ga shi, ni'imar ƙasar za ta nisancimazauninka,Raɓar samaniya can ƙwanƙoli zata nisance ka.
40 Ta wurin takobinka za ka rayuZa ka yi wa ɗan'uwanka barantaka,Amma sa'ad da ka ɓalle,Za ka kakkarye karkiyarsa dagawuyanka.”
41 Isuwa dai ya ƙi jinin Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Sai Isuwa ya ce a ransa, “Kwanakin makoki domin mahaifina suna gabatowa, sa'an nan zan kashe Yakubu ɗan'uwana.”
42 Amma maganganun Isuwa babban ɗanta suka kai a kunnen Rifkatu. Saboda haka, sai ta aika aka kirawo Yakubu ƙaramin ɗanta. Ta ce masa, “Ga shi, ɗan'uwanka Isuwa, yana ta'azantar da kansa da nufin ya kashe ka, ya ɗau fansa.