1 Ishaku ya kira Yakubu ya sa masa albarka, ya umarce shi da cewa, “Ba za ka auri ɗaya daga cikin 'ya'yan matan Kan'aniyawa ba.
2 Tashi, ka tafi Fadan-aram, zuwa gidan Betuwel kakanka na wajen uwa, ka zaɓo wa kanka mata daga cikin 'ya'ya mata na Laban ɗan'uwan mahaifiyarka a can.
3 Allah Maɗaukaki ya sa maka albarka, ya sa ka hayayyafa ya riɓaɓɓanya ka, ka zama ƙungiyar jama'o'i,
4 ya kuma sa ka sami albarkar Ibrahim da zuriyarka tare da kai, har da za ka amshe ƙasar baƙuncinka wadda Allah ya bai wa Ibrahim!”
5 Da haka, Ishaku ya sallami Yakubu, ya kuwa tafi Fadan-aram wurin Laban, ɗan Betuwel Ba'aramiye ɗan'uwan Rifkatu, mahaifiyar Yakubu da Isuwa.