3 Allah Maɗaukaki ya sa maka albarka, ya sa ka hayayyafa ya riɓaɓɓanya ka, ka zama ƙungiyar jama'o'i,
4 ya kuma sa ka sami albarkar Ibrahim da zuriyarka tare da kai, har da za ka amshe ƙasar baƙuncinka wadda Allah ya bai wa Ibrahim!”
5 Da haka, Ishaku ya sallami Yakubu, ya kuwa tafi Fadan-aram wurin Laban, ɗan Betuwel Ba'aramiye ɗan'uwan Rifkatu, mahaifiyar Yakubu da Isuwa.
6 Yanzu Isuwa ya ga Ishaku ya sa wa Yakubu albarka, ya kuwa sallame shi zuwa Fadan-aram domin ya auro mace daga can. Da Isuwa ya ga Ishaku ya sa wa Yakubu albarka ya kuma umarce shi da cewa, “Ba za ka auro wata daga cikin 'yan matan Kan'aniyawa ba,”
7 ya kuma ga Yakubu ya biye wa mahaifinsa da mahaifiyarsa, har ya tafi Fadan-aram,
8 sai Isuwa ya gane 'yan matan Kan'aniyawa ba su gamshi Ishaku mahaifinsa ba.
9 Saboda haka Isuwa ya tafi wurin Isma'ilu ya auro Mahalat 'yar'uwar Nebayot, 'yar Isma'ilu ɗan Ibrahim, banda matan da yake da su.