15 Laban kuwa ya ce wa Yakubu, “Don kana dangina, za ka yi mini barantaka a banza? Ka faɗa mini, nawa zan biya ka?”
16 Laban dai yana da 'ya'ya mata biyu, sunan babbar Lai'atu, sunan ƙaramar kuwa Rahila.
17 Lai'atu dai ba kyakkyawa ba ce, amma Rahila kyakkyawa ce, dirarriya.
18 Yakubu ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce wa Laban, “Zan yi maka barantaka shekara bakwai domin 'yarka Rahila.”
19 Laban ya ce, “Gara in ba ka ita da in ba wani dabam, zauna tare da ni.”
20 Saboda haka, ya yi barantaka shekara bakwai domin Rahila, amma a ganinsa kamar 'yan kwanaki ne saboda ƙaunar da yake mata.
21 Yakubu ya ce wa Laban, “Ba ni matata domin in shiga wurinta, domin lokacin da muka shirya ya cika.”