18 Yakubu ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce wa Laban, “Zan yi maka barantaka shekara bakwai domin 'yarka Rahila.”
19 Laban ya ce, “Gara in ba ka ita da in ba wani dabam, zauna tare da ni.”
20 Saboda haka, ya yi barantaka shekara bakwai domin Rahila, amma a ganinsa kamar 'yan kwanaki ne saboda ƙaunar da yake mata.
21 Yakubu ya ce wa Laban, “Ba ni matata domin in shiga wurinta, domin lokacin da muka shirya ya cika.”
22 Sai Laban ya tattara mutanen wurin duka, ya yi biki.
23 Amma da maraice, ya ɗauki 'yarsa Lai'atu ya kawo ta wurin Yakubu, Yakubu ya shiga a wurinta.
24 (Laban ya ba 'yarsa Lai'atu Zilfa ta zama kuyangarta).