24 (Laban ya ba 'yarsa Lai'atu Zilfa ta zama kuyangarta).
25 Da gari ya waye kuma ga shi, ashe, Lai'atu ce. Sai Yakubu ya ce wa Laban, “Mene ne wannan da ka yi mini? Ba don Rahila na yi maka barantaka ba? Don me ka yaudare ni?”
26 Laban ya ce, “A nan wurinmu ba a yin haka, a aurar da ƙarama kafin 'yar fari.
27 Ka jira, bayan kwana bakwai na lokacin auren sun wuce, sa'an nan za mu ba ka Rahila saboda barantakar da za ka yi mini shekara bakwai nan gaba.”
28 Yakubu kuwa ya yi haka ɗin, ya cikasa makon, sa'an nan Laban ya aurar masa da 'yarsa Rahila.
29 (Laban ya ba 'yarsa Rahila Bilha, kuyangarsa, ta zama kuyangarta).
30 Sai Yakubu ya shiga wurin Rahila, amma ya fi ƙaunar Rahila da Lai'atu. Ya yi wa Laban barantaka waɗansu shekara bakwai kuma.