26 Laban ya ce, “A nan wurinmu ba a yin haka, a aurar da ƙarama kafin 'yar fari.
27 Ka jira, bayan kwana bakwai na lokacin auren sun wuce, sa'an nan za mu ba ka Rahila saboda barantakar da za ka yi mini shekara bakwai nan gaba.”
28 Yakubu kuwa ya yi haka ɗin, ya cikasa makon, sa'an nan Laban ya aurar masa da 'yarsa Rahila.
29 (Laban ya ba 'yarsa Rahila Bilha, kuyangarsa, ta zama kuyangarta).
30 Sai Yakubu ya shiga wurin Rahila, amma ya fi ƙaunar Rahila da Lai'atu. Ya yi wa Laban barantaka waɗansu shekara bakwai kuma.
31 Sa'ad da Ubangiji ya ga ana ƙin Lai'atu, ya buɗe mahaifarta, amma Rahila bakarariya ce.
32 Lai'atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra'ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.”