3 A sa'ad da garkunan suka tattaru a wurin, makiyayan sukan kawar da dutsen daga bakin rijiyar, su shayar da su, sa'an nan su mayar da dutsen a wurinsa, a bisa bakin rijiya.
4 Yakubu ya ce musu, “'Yan'uwana, daga ina kuka fito?”Suka ce, “Daga Haran muke.”
5 Sai ya ce musu, “Kun san Laban ɗan Nahor?”Suka ce, “Mun san shi.”
6 Ya ce musu, “Lafiyarsa ƙalau?”Suka ce, “I, lafiya ƙalau yake, ga ma Rahila 'yarsa, tana zuwa da bisashensa!”
7 Ya ce, “Ga shi kuwa, da sauran rana da yawa, lokacin tattaruwar dabbobi bai yi ba, me zai hana ku shayar da tumakin, ku sāke kai su wurin kiwo?”
8 Amma suka ce, “Ba za mu iya ba, sai sauran garkunan duka sun taru, sa'an nan a kawar da dutsen daga bakin rijiyar, sa'an nan mu shayar da garkuna.”
9 Kafin ya rufe baki, sai ga Rahila ta zo da bisashen mahaifinta, gama ita take kiwonsu.