18 “Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za ta ba ka, za ka kuwa ci ganyayen saurar.
19 Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.”2Tas 3.10; Far 2.7; Zab 90.3; 104.29; M. Had 12.7)
20 Mutumin ya sa wa matarsa suna Hawwa'u, domin ita ce uwar 'yan adam.
21 Ubangiji Allah kuwa ya yi wa mutumin da matarsa tufafi na fata, ya suturce su.
22 Sa'an nan Ubangiji Allah ya ce, “Ga shi, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya miƙa hannunsa ya ɗiba daga cikin itacen rai ɗin nan, ya ci, ya rayu har abada.”
23 Domin haka Ubangiji Allah ya fisshe shi daga cikin gonar Aidan, ya noma ƙasa, wato inda aka ɗauko shi.
24 Ya kori mutum kuma a gabashin gonar Aidan, ya kafa kerubobi, da kuma takobi mai harshen wuta wanda yake jujjuyawa ko'ina don su tsare hanya zuwa itacen rai.