1 Sa'ad da Rahila ta ga ba ta haihuwa, sai ta ji kishin 'yar'uwarta, ta kuma ce wa Yakubu, “Ka ba ni 'ya'ya, in kuwa ba haka ba, zan mutu!”
2 Fushin Yakubu ya yi ƙuna a kan Rahila, ya ce, “Ina daidai da Allah ne, wanda ya hana ki haihuwa?.”
3 Sai ta ce, “Ga kuyangata Bilha, ka shiga wurinta, domin ta haihu bisa gwiwoyina, domin ni ma in sami 'ya'ya ta wurinta.”
4 Don haka ta ba shi Bilha ta zama matarsa. Yakubu kuwa ya shiga wurinta.
5 Bilha kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa.
6 Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni, ya ji muryata, ya kuwa ba ni ɗa.” Saboda haka ta raɗa masa suna Dan.
7 Bilha, kuyangar Rahila, ta sāke yin ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa na biyu.