23 Ta yi ciki ta haifa ɗa, ta ce, “Allah ya kawar da zargina,”
24 ta sa masa suna Yusufu, tana cewa, “Da ma a ce Ubangiji ya ƙara mini wani ɗa!”
25 Bayan da Rahila ta haifi Yusufu, Yakubu ya ce wa Laban, “Ka sallame mu, domin mu tafi gidanmu a ƙasarmu.
26 Ka ba ni matana da 'ya'yana waɗanda na yi maka barantaka saboda su, ka bar mu mu tafi, ka dai san ɗawainiyar da na yi maka.”
27 Amma Laban ya ce masa, “Da za ka yarda mini, sai in ce, na fahimta bisa ga istihara, cewa Ubangiji ya sa mini albarka saboda kai.
28 Ka faɗa mini ladanka in ba ka.”
29 Yakubu ya ce masa, “Kai da kanka ka san barantakar da na yi maka, yadda bisashenka suka yawaita a hannuna.