32 bar ni, in ratsa garkenka duka yau, in keɓe dukan masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki, waɗannan ne za su zama ladana.
33 Ta haka amincina zai shaide ni a gabanka a sa'ad da ka zo bincike hakkina. Duk wanda aka iske ba dabbare-dabbare ba ne, kuma ba babare-babare ba ne cikin awaki, ba kuma baƙi ba ne a cikin raguna, in aka samu a wurina, sai a ɗauka, na sata ne.”
34 Laban ya ce, “Madalla! Bari ya kasance kamar yadda ka faɗa.”
35 Amma a ran nan Laban ya ware bunsuran da suke dabbare-dabbare da masu sofane, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare da kyalloli, da dukan baƙaƙen tumaki, ya danƙa su a hannun 'ya'yansa maza,
36 ya sa nisan tafiya ta kwana uku tsakaninsu da Yakubu, Yakubu kuma ya ci gaba da kiwon sauran garken Laban.
37 Yakubu ya samo ɗanyun tsabgogin aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bayyanar da fararen zane-zanensu a fili.
38 Ya kafa tsabgogin da ya ɓare a gaban garkuna a magudana, wato kwamame na banruwa, don sukan yi barbara a wurin sa'ad da suka zo shan ruwa.