1 Yakubu ya ji 'ya'yan Laban suna cewa, “Yakubu ya kwashe dukan abin da yake na mahaifinmu, daga cikin dukan abin da yake na mahaifinmu kuma ya sami dukiyarsa.”
2 Yakubu kuma ya ga ba shi da farin jini a wurin Laban kamar dā.
3 Ubangiji ya ce wa Yakubu, “Ka koma ƙasar kakanninka da danginka, ni kuwa ina tare da kai.”
4 Saboda haka Yakubu ya aika a kirawo Rahila da Lai'atu zuwa cikin saura inda garkensa yake,
5 ya ce musu, “Na ga ba ni da sauran farin jini wurin mahaifinku kamar dā. Amma Allah na mahaifina yana tare da ni.