13 Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa dutsen mai, ka kafa shi al'amudi, ka kuma rantse mini. Yanzu fa tashi ka fita daga cikin ƙasan nan, ka koma ƙasar haihuwarka.’ ”
14 Rahila da Lai'atu suka amsa masa, “Akwai wani rabo, ko gādon da ya rage mana a cikin gidan mahaifinmu?
15 Ba ga shi ma, sai kamar baƙi yake ɗaukarmu ba? Gama ya sayar da mu, yana kuwa morar kuɗin da aka bayar dominmu.
16 Dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga wurin mahaifinmu, tamu ce da 'ya'yanmu, yanzu fa, kome Allah ya faɗa maka, sai ka yi.”
17 Sai Yakubu ya tashi, ya ɗauki 'ya'yansa, da matansa a bisa raƙumansa,
18 ya kora shanunsa duka, da dukan bisashen da ya samu, da shanu da suke nasa, waɗanda ya samu a Fadan-aram a ƙasar Mesofotamiya, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mahaifinsa Ishaku.
19 Amma a sa'an nan Laban ya riga ya tafi ya yi wa tumakinsa sausaya, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta.