17 Sai Yakubu ya tashi, ya ɗauki 'ya'yansa, da matansa a bisa raƙumansa,
18 ya kora shanunsa duka, da dukan bisashen da ya samu, da shanu da suke nasa, waɗanda ya samu a Fadan-aram a ƙasar Mesofotamiya, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mahaifinsa Ishaku.
19 Amma a sa'an nan Laban ya riga ya tafi ya yi wa tumakinsa sausaya, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta.
20 Yakubu kuwa ya yaudari Laban Ba'aramiye da bai sanar da shi zai gudu ba.
21 Ya gudu da dukan abin da yake da shi, ya tashi ya haye Yufiretis, ya miƙe zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai.
22 Sa'ad da aka sanar da Laban, cewa Yakubu ya gudu da kwana uku,
23 sai ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi sawunsa har kwana bakwai, yana biye da shi kurkusa har zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai.