1 Yakubu ya yi tafiyarsa, mala'ikun Allah kuma suka gamu da shi.
2 Sa'ad da Yakubu ya gan su ya ce, “Waɗannan rundunar Allah ce!” Saboda haka ya sa wa wannan wuri suna Mahanayim.
3 Yakubu kuwa ya aiki jakadu a gabansa zuwa wurin Isuwa ɗan'uwansa a cikin ƙasar Seyir a karkarar Edom,
4 yana umartarsu da cewa, “Haka za ku faɗa wa shugabana Isuwa, ‘Ga abin da baranka Yakubu ya ce, “Na yi baƙunta a ƙasar Laban, na zauna har wa yau.
5 Ina da takarkarai, da jakai, da garkuna, da barori mata da maza, na kuwa aika a faɗa wa shugabana domin in sami tagomashi a idonka.” ’ ”
6 Jakadun kuwa suka komo wurin Yakubu, suka ce, “Mun je wurin ɗan'uwanka Isuwa, yana kuwa zuwa ya tarye ka da mutum arbaminya tare da shi.”
7 Yakubu fa ya tsorata ƙwarai, ya damu, sai ya karkasa mutanen da suke tare da shi, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu, da raƙuma cikin ƙungiya biyu,