1 Yanzu fa Dinatu 'yar Lai'atu, wadda ta haifa wa Yakubu, ta fita ta ziyarci waɗansu matan ƙasar,
2 sai Shekem, ɗan Hamor Bahiwiye, yariman ƙasar, da ya gan ta, ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.
3 Ransa kuwa ya zaƙu da son Dinatu 'yar Yakubu. Ya ƙaunaci budurwar, ya kalallame ta da maganganu masu daɗi.
4 Sai Shekem ya yi magana da mahaifinsa, Hamor, ya ce, “Ka auro mini wannan budurwa ta zama matata.”
5 Yakubu kuwa ya ji an ɓata 'yarsa, Dinatu, amma 'ya'yansa maza suna tare da garken cikin saura, saboda haka Yakubu ya yi shiru har kafin su komo.
6 Sai Hamor mahaifin Shekem ya fita ya je wurin Yakubu, ya yi magana da shi.