18 Da tana suma, sai ta sa masa suna Ben-oni, amma mahaifinsa ya sa masa suna Biliyaminu.
19 Ta haka fa Rahila ta rasu, aka kuwa binne ta a bakin hanya zuwa Efrata, wato Baitalami.
20 Yakubu ya kafa al'amudi bisa kabarinta, al'amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.
21 Isra'ila ya ci gaba da tafiyarsa, ya kuwa kafa alfarwarsa daura da hasumiyar Eder.
22 A lokacin da Isra'ila yake zaune a ƙasar, Ra'ubainu ya je ya kwana da Bilha kwarkwarar mahaifinsa, Isra'ila kuwa ya sami labari.'Ya'yan Isra'ila, maza, su goma sha biyu ne.
23 'Ya'yan Lai'atu, su ne Ra'ubainu ɗan farin Yakubu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, da Issaka, da Zabaluna.
24 'Ya'yan Rahila, su ne Yusufu da Biliyaminu.