21 Isra'ila ya ci gaba da tafiyarsa, ya kuwa kafa alfarwarsa daura da hasumiyar Eder.
22 A lokacin da Isra'ila yake zaune a ƙasar, Ra'ubainu ya je ya kwana da Bilha kwarkwarar mahaifinsa, Isra'ila kuwa ya sami labari.'Ya'yan Isra'ila, maza, su goma sha biyu ne.
23 'Ya'yan Lai'atu, su ne Ra'ubainu ɗan farin Yakubu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, da Issaka, da Zabaluna.
24 'Ya'yan Rahila, su ne Yusufu da Biliyaminu.
25 'Ya'yan Bilha, kuyangar Rahila, su ne Dan da Naftali.
26 'Ya'yan Zilfa, kuyangar Lai'atu, su ne Gad da Ashiru. Waɗannan su ne 'ya'yan Yakubu da aka haifa masa a Fadan-aram.
27 Yakubu kuma ya zo wurin mahaifinsa a Mamre, a Kiriyat-arba, wato Hebron ke nan, inda Ibrahim da Ishaku suka yi baƙunci.