1 Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, wato Edom.
2 Isuwa ya auri matansa daga cikin Kan'aniyawa, wato Ada 'yar Elon Bahitte, da Oholibama 'yar Ana ɗan Zibeyon Bahiwiye,
3 da Basemat, 'yar Isma'ilu, 'yar'uwar Nebayot.
4 Ada ta haifa wa Isuwa, Elifaz, Basemat kuma ta haifi Reyuwel.
5 Oholibama ta haifi Yewush, da Yalam, da Kora. Waɗannan su ne 'ya'yan Isuwa waɗanda aka haifa masa a ƙasar Kan'ana.