24 Waɗannan su ne 'ya'yan Zibeyon, maza, Aiya da Ana. Shi ne Ana wanda ya sami maɓuɓɓugan ruwan zafi a cikin jeji, a sa'ad da yake kiwon jakunan mahaifinsa Zibeyon.
25 Waɗannan su ne 'ya'yan Ana, Dishon da Oholibama 'yar Ana.
26 Waɗannan su ne 'ya'yan Dishon, maza, Hemdan da Eshban, da Yitran, da Keran.
27 Waɗannan su ne 'ya'yan Ezer, maza, Bilhan, da Zayawan, da Akan.
28 Waɗannan su ne 'ya'yan Dishan, maza, Uz da Aran.
29 Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, shugaba Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana,
30 da Dishon, da Ezer, da Dishan, waɗannan su ne shugabannin Horiyawa bisa ga shugabancinsu a ƙasar Seyir.