29 Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, shugaba Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana,
30 da Dishon, da Ezer, da Dishan, waɗannan su ne shugabannin Horiyawa bisa ga shugabancinsu a ƙasar Seyir.
31 Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a ƙasar Edom, kafin wani sarki ya taɓa yin mulkin Isra'ilawa.
32 Bela ɗan Beyor ya yi sarautar Edom, sunan birninsa kuwa Dinhaba.
33 Bela ya rasu, sai Yobab ɗan Zera daga Bozara ya ci sarauta a bayansa.
34 Ɗan Yobab ya rasu, sai Husham na ƙasar Temanawa ya ci sarauta a bayansa.
35 Da Husham ya rasu, sai Hadad ɗan Bedad wanda ya ci Madayana a ƙasar Mowab, ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa kuwa Awit ne.