32 Bela ɗan Beyor ya yi sarautar Edom, sunan birninsa kuwa Dinhaba.
33 Bela ya rasu, sai Yobab ɗan Zera daga Bozara ya ci sarauta a bayansa.
34 Ɗan Yobab ya rasu, sai Husham na ƙasar Temanawa ya ci sarauta a bayansa.
35 Da Husham ya rasu, sai Hadad ɗan Bedad wanda ya ci Madayana a ƙasar Mowab, ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa kuwa Awit ne.
36 Da Hadad ya rasu, sai Samla na Masreka ya ci sarauta a bayansa.
37 Da Samla ya rasu, sai Shawul na Rehobot ta Yufiretis ya ci sarauta a bayansa.
38 Da Shawul ya rasu, sai Ba'al-hanan ɗan Akbor ya ci sarauta a bayansa.