1 Yakubu ya zauna a ƙasar Kan'ana inda mahaifinsa ya yi baƙunci.
2 Wannan shi ne tarihin zuriyar Yakubu.Yusufu yana da shekara goma sha bakwai sa'ad da ya zama makiyayin garke tare da 'yan'uwansa, ɗan ƙanƙanen yaro ne a tsakanin 'ya'ya maza na Bilha da Zilfa matan mahaifinsa. Sai Yusufu ya kawo labarin munanan abubuwa da 'yan'uwansa suke yi a wurin mahaifinsa,
3 Isra'ila kuwa ya fi ƙaunar Yusufu da kowannensu, domin shi ɗan tsufansa ne. Sai ya yi masa riga mai ado.
4 Amma sa'ad da 'yan'uwansa suka gane mahaifinsu yana ƙaunarsa fiye da dukansu, suka ƙi jininsa, ba su iya maganar alheri da shi.
5 Yusufu ya yi mafarki. Sa'ad da ya faɗa wa 'yan'uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.