22 Kada mu kashe shi, mu dai jefa shi cikin rijiyan nan a jeji, amma kada mu yi masa lahani.” Ya yi haka da nufin ya cece shi daga hannunsu, ya mayar da shi ga mahaifinsu.
23 Don haka, sa'ad da Yusufu ya zo wurin 'yan'uwansa, suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai ado wadda take wuyansa.
24 Suka ɗauke shi suka jefa shi cikin rijiyar. Rijiyar kuwa wofi ce, ba ruwa a ciki.
25 Suka zauna su ci abinci, da suka ɗaga ido suka duba, sai ga ayarin Isma'ilawa suna zuwa daga Gileyad, da raƙumansu ɗauke da ƙāro, da man ƙanshi na wartsakewa, da mur, suna gangarawa kan hanyarsu zuwa Masar.
26 Yahuza ya ce wa 'yan'uwansa, “Wace riba ke nan, in mun kashe ɗan'uwanmu, muka ɓoye jininsa?
27 Ku zo mu sayar da shi ga Isma'ilawa, kada mu bar hannunmu ya taɓa shi, gama shi ɗan'uwanmu ne, shi kuma jikinmu ne.” 'Yan'uwansa suka yarda da shi.
28 Da Madayanawa, fatake, suna wucewa, sai suka jawo Yusufu suka fitar da shi daga cikin rijiyar suka sayar wa Isma'ilawa a bakin azurfa ashirin, aka kuwa tafi da Yusufu zuwa Masar.