13 Da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu, ya fita waje,
14 sai ta yi kira ga mutanen gidan, ta ce musu, “Ku duba ku gani, ya kawo mana Ba'ibrane ya ci mutuncinmu. Ya zo wurina don ya kwana da ni, sai na yi ihu da ƙarfi.
15 Da ya ji na ta da murya na yi ihu, ya kuwa gudu ya bar rigarsa, ya fita waje.”
16 Ta ajiye rigar a wurinta har maigidansa ya komo.
17 Sai ta mayar masa da magana, ta ce, “Baran nan, Ba'ibrane wanda ka kawo cikinmu, ya shigo wurina don ya ci mutuncina,
18 amma nan da nan da na ta da murya na yi ihu, sai ya gudu ya bar rigarsa a hannuna, ya gudu zuwa waje.”
19 Sa'ad da maigidan Yusufu ya ji abin da matarsa ta faɗa masa, “Ka ji yadda baranka ya yi da ni ke nan,” sai ya husata.