16 Ta ajiye rigar a wurinta har maigidansa ya komo.
17 Sai ta mayar masa da magana, ta ce, “Baran nan, Ba'ibrane wanda ka kawo cikinmu, ya shigo wurina don ya ci mutuncina,
18 amma nan da nan da na ta da murya na yi ihu, sai ya gudu ya bar rigarsa a hannuna, ya gudu zuwa waje.”
19 Sa'ad da maigidan Yusufu ya ji abin da matarsa ta faɗa masa, “Ka ji yadda baranka ya yi da ni ke nan,” sai ya husata.
20 Maigidan Yusufu ya ɗauke shi ya māka shi a kurkuku, inda 'yan sarƙa na sarki suke tsare, can ya zauna a kurkuku.
21 Amma Ubangiji yana tare da Yusufu, ya kuwa nuna masa madawwamiyar ƙauna, ya sa ya sami farin jini a wurin yarin kurkukun.
22 Yarin kurkuku ya shugabantar da Yusufu bisa dukan 'yan sarƙa da suke a kurkuku, dukan abin da ake yi a wurin kuma shi yake yi.