8 Kayinu ya ce wa ɗan'uwansa Habila, “Mu tafi cikin saura.” A lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa ɗan'uwansa Habila, har ya kashe shi.
9 Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan'uwanka?”Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan'uwana ne?”
10 Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan'uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa.
11 Yanzu fa, kai la'ananne ne daga cikin ƙasar da ta buɗe baki, ta karɓi jinin ɗan'uwanka daga hannunka.
12 In ka yi noma, ƙasar ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta ba, za ka zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya.”
13 Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Hukuncina ya fi ƙarfina.
14 Ga shi, yanzu ka kore ni a guje daga fuskar ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”