2 Fir'auna ya yi fushi da ma'aikatan nan nasa biyu, wato shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya.
3 Ya ba da su a sa su kurkuku, cikin gidan shugaban masu tsaron fāda, wato kurkuku inda Yusufu yake a tsare.
4 Shugaban 'yan tsaron ya danƙa su ga Yusufu don ya hidimta musu, sun kuwa jima a kurkukun har an daɗe.
5 Suka yi mafarki, su biyu ɗin, a dare ɗaya, da shi mai shayarwar da mai tuyar na gidan Sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, kowanne kuwa da nasa mafarkin da kuma tasa irin fassarar mafarkin.
6 Da Yusufu ya zo wurinsu da safe, ya ga sun damu.
7 Sai ya tambaye su ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a yamutse yau?”
8 Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.”Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”