20 A rana ta uku, wadda take ranar haihuwar Fir'auna, Fir'auna ya yi wa dukan bayinsa biki, sai ya kawo shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya a gaban fādawansa.
21 Ya komar da shugaban masu shayarwa a matsayinsa na shayarwa, ya kuwa miƙa finjali a hannun Fir'auna,
22 amma ya rataye shugaban masu tuya kamar yadda Yusufu ya fassara musu.
23 Duk da haka shugaban masu shayarwar bai tuna da Yusufu ba, amma ya manta da shi.