6 Da Yusufu ya zo wurinsu da safe, ya ga sun damu.
7 Sai ya tambaye su ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a yamutse yau?”
8 Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.”Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”
9 Saboda haka, shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusufu mafarkinsa, ya ce masa, “A mafarkina ga kurangar inabi a gabana.
10 A kurangar akwai rassa uku. Sai ta yi toho, ta huda nan da nan, ta kuma yi nonna, har suka nuna suka zama inabi.
11 Finjalin Fir'auna na hannuna, sai na ɗauki 'ya'yan inabi na matse su cikin finjalin Fir'auna, na sa finjalin a hannun Fir'auna.”
12 Yusufu ya ce masa, “Wannan ita ce fassararsa, rassan nan uku, kwana uku ne,