1 Bayan shekaru biyu cif, Fir'auna ma ya yi mafarki, ga shi, yana tsaye a bakin kogin Nilu,
2 sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul suka fito daga Nilu, suka yi kiwo cikin iwa.
3 Ga kuma waɗansu shanu bakwai munana ramammu suka fito daga cikin Nilu a bayansu, suka tsaya kusa da waɗancan shanu a bakin Nilu.
4 Sai shanun nan munana ramammu suka cinye shanun nan bakwai masu sheƙi, masu ƙibar. Sai Fir'auna ya farka.
5 Barci kuma ya kwashe shi, ya sāke yin mafarki a karo na biyu, sai zangarku bakwai masu kauri kyawawa suna girma a kara gudu.
6 Ga shi kuma, a bayansu waɗansu zangarku bakwai suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar.
7 Sai siraran zangarkun suka haɗiye zangarkun nan bakwai masu kauri kyawawa. Sai Fir'auna ya farka, ashe, mafarki ne.