16 Yusufu ya amsa wa Fir'auna ya ce, “Ba a gare ni ba, Allah zai amsa wa Fir'auna da kyakkyawar amsa.”
17 Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, a cikin mafarkina ina tsaye a bakin Kogin Nilu,
18 ga shanu bakwai, masu sheƙi masu ƙiba suka fito daga cikin Nilu suna kiwo cikin iwa.
19 Sai waɗansu shanu bakwai ƙanjamammu, munana, ramammu, irin waɗanda ban taɓa ganinsu a ƙasar Masar ba, suka fito bayansu.
20 Sai ramammun, munanan shanun suka cinye shanun nan bakwai masu ƙiba na farko,
21 amma da suka haɗiye su, ba wanda zai iya sani sun haɗiye su, gama suna nan a ramammunsu kamar yadda suke a dā. Sai na farka.
22 Har yanzu kuma, a cikin mafarkina ga zangarku masu kauri kyawawa guda bakwai, suna girma a kara guda,