29 Za a yi shekara bakwai cike da ƙoshi a ƙasar Masar duka,
30 amma a bayansu za a yi shekara bakwai na yunwa, amma za a manta da dukan ƙoshin nan a ƙasar Masar, yunwar kuwa za ta game dukan ƙasar.
31 Zai kuwa zama kamar ba a taɓa yin ƙoshi a ƙasar ba, saboda tsananin yunwar.
32 Maimaitawar mafarkin nan na Fir'auna kuwa, ya nuna cewa Allah ya riga ya ƙaddara al'amarin, hakika kuwa Allah zai tabbatar da shi ba da jimawa ba.
33 “Yanzu fa bari Fir'auna ya zaɓi mutum mai basira, mai hikima, ya sa shi bisa ƙasar Masar.
34 Bari Fir'auna ya ci gaba da naɗa shugabanni bisa ƙasa, don su tattara humushin amfanin ƙasar Masar na shekarun nan bakwai na ƙoshi.
35 Bari kuma su tattara dukan abinci a shekarun nan bakwai masu zuwa na albarka, su tsiba a ƙarƙashin ikon Fir'auna saboda abinci cikin birane, su kuma lura da shi.