6 Ga shi kuma, a bayansu waɗansu zangarku bakwai suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar.
7 Sai siraran zangarkun suka haɗiye zangarkun nan bakwai masu kauri kyawawa. Sai Fir'auna ya farka, ashe, mafarki ne.
8 Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir'auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su.
9 Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir'auna, “Yau, na tuna da laifofina.
10 Sa'ad da ka yi fushi da barorinka, ka sa ni da shugaban masu tuya cikin kurkukun da yake a cikin gidan shugaban masu tsaron fāda,
11 muka yi mafarki dare ɗaya, ni da shi, kowane mutum da irin tasa fassarar mafarkin.
12 Akwai wani Ba'ibrane, ɗan saurayi, tare da mu, bawan shugaban masu tsaron fāda, sa'ad da muka faɗa masa sai ya fassara mana mafarkanmu, ya yi wa kowannenmu fassara bisa kan mafarkinsa.