1 A sa'ad da Yakubu ya ji akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa 'ya'yansa maza, “Me ya sa kuke zuba wa juna ido?
2 Ga shi kuwa, na ji akwai hatsi a Masar, ku gangara ku sayo mana hatsi a can domin mu rayu, kada mu mutu.”
3 Don haka 'yan'uwan Yusufu su goma suka gangara su sayo hatsi a Masar.
4 Amma Yakubu bai aiki Biliyaminu ɗan'uwan Yusufu tare da 'yan'uwansa ba, gama ya ce, “Kada wata ɓarna ta same shi.”
5 Haka nan 'ya'yan Isra'ila maza suka zo su sayi hatsi tare da sauran matafiya, gama ana yunwa a ƙasar Kan'ana.