3 Don haka 'yan'uwan Yusufu su goma suka gangara su sayo hatsi a Masar.
4 Amma Yakubu bai aiki Biliyaminu ɗan'uwan Yusufu tare da 'yan'uwansa ba, gama ya ce, “Kada wata ɓarna ta same shi.”
5 Haka nan 'ya'yan Isra'ila maza suka zo su sayi hatsi tare da sauran matafiya, gama ana yunwa a ƙasar Kan'ana.
6 Yanzu fa, Yusufu shi ne mai mulkin ƙasar, shi ne kuwa mai sayar wa jama'ar ƙasar duka. 'Yan'uwan Yusufu suka zo suka sunkuya har ƙasa a gabansa.
7 Da Yusufu ya ga 'yan'uwansa, ya gane da su, amma ya mai da su kamar baƙi, ya yi musu magana da gautsi ya ce, “Daga ina kuka fito?”Suka ce, “Daga ƙasar Kan'ana muka zo sayen abinci.”
8 Yusufu kuwa ya gane da 'yan'uwansa amma su ba su gane shi ba.
9 Sai Yusufu ya tuna da mafarkan da ya yi a kansu, ya ce musu, “Ku magewaya ne, zuwa kuka yi domin ku leƙi asirin ƙasar.”