7 Da Yusufu ya ga 'yan'uwansa, ya gane da su, amma ya mai da su kamar baƙi, ya yi musu magana da gautsi ya ce, “Daga ina kuka fito?”Suka ce, “Daga ƙasar Kan'ana muka zo sayen abinci.”
8 Yusufu kuwa ya gane da 'yan'uwansa amma su ba su gane shi ba.
9 Sai Yusufu ya tuna da mafarkan da ya yi a kansu, ya ce musu, “Ku magewaya ne, zuwa kuka yi domin ku leƙi asirin ƙasar.”
10 Suka ce masa, “A'a, shugabanmu, domin sayen abinci bayinka suka zo.
11 Mu duka 'ya'yan mutum guda ne, amintattu kuma, bayinka ba magewaya ba ne.”
12 Yusufu ya ce musu, “A'a! Ku dai kun zo ku ga inda ƙasarmu yake da rashin ƙarfi.”
13 Suka ce, “Mu bayinka, 'yan'uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, 'ya'yan mutum guda a ƙasar Kan'ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.”