9 Sai Yusufu ya tuna da mafarkan da ya yi a kansu, ya ce musu, “Ku magewaya ne, zuwa kuka yi domin ku leƙi asirin ƙasar.”
10 Suka ce masa, “A'a, shugabanmu, domin sayen abinci bayinka suka zo.
11 Mu duka 'ya'yan mutum guda ne, amintattu kuma, bayinka ba magewaya ba ne.”
12 Yusufu ya ce musu, “A'a! Ku dai kun zo ku ga inda ƙasarmu yake da rashin ƙarfi.”
13 Suka ce, “Mu bayinka, 'yan'uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, 'ya'yan mutum guda a ƙasar Kan'ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.”
14 Amma Yusufu ya ce musu, “Ai, kamar dai yadda na faɗa muku, magewaya ne ku.
15 Ta haka za a jarraba ku, da ran Fir'auna, ba za ku fita daga nan wurin ba, sai autanku ya zo nan.