22 ga waɗansu kuɗin kuma mun riƙo a hannunmu, mun gangaro mu ƙara sayen abinci. Ba mu san wanda ya sa kuɗin nan namu a tayakanmu ba.”
23 Ya amsa ya ce, “Salama na tare da ku, kada ku ji tsoro, Allahnku da Allah na mahaifinku ne kaɗai ya sa muku dukiyar cikin tayakanku. Na karɓi kuɗinku.” Sai ya fito musu da Saminu.
24 Da mutumin ya kawo su gidan Yusufu, ya ba su ruwa, suka kuwa wanke ƙafafunsu, sa'an nan kuma ya bai wa jakunansu tauna,
25 sai suka shirya tsarabar, domin Yusufu yana zuwa da tsakar rana, saboda sun ji, wai zai ci abinci a nan.
26 Sa'ad da Yusufu ya koma gida, suka kawo tsarabar da suka riƙo masa cikin gida, suka sunkuya har ƙasa a gabansa.
27 Ya tambayi lafiyarsu ya ce, “Mahaifinku yana lafiya, tsohon nan da kuka yi magana a kansa? Yana nan da rai?”
28 Sai suka amsa, “Bawanka, mahaifinmu yana lafiya, har yanzu yana da rai.” Suka sunkuya suka yi masa mubaya'a.