1 Isra'ila ya kama tafiyarsa da dukan abin da yake da shi. Ya zo Biyer-sheba, ya kuwa ba da hadayu ga Allah na mahaifinsa Ishaku.
2 Sai Allah ya yi magana cikin wahayin dare, ya ce, “Yakubu.”Ya amsa ya ce, “Na'am.”
3 Sai ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama a can zan maishe ka babbar al'umma.
4 Ni kuwa zan gangara tare da kai zuwa Masar, ni kuma zan sāke haurowa tare da kai. Lokacin mutuwarka za ka mutu a hannun Yusufu.”
5 Sai Yakubu ya tashi daga Biyer-sheba, 'ya'yan Isra'ila maza kuwa suka ɗauki mahaifinsu Yakubu, da 'yan ƙananansu da matansu a cikin kekunan shanun da Fir'auna ya aika a ɗauko su.
6 Suka kuma kora shanunsu, suka ɗauki kayayyakinsu waɗanda suka samu a ƙasar Kan'ana, suka iso Masar, Yakubu da zuriyarsa duka,
7 'ya'yansa maza da jikokinsa maza tare da shi, 'ya'yansa mata, da jikokinsa mata, ya kawo zuriyarsa dukka zuwa ƙasar Masar.