19 'Ya'ya maza, na Rahila, matar Yakubu, su ne Yusufu da Biliyaminu.
20 Asenat 'yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusufu Manassa da Ifraimu a ƙasar Masar.
21 'Ya'yan Biliyaminu, maza, su ne Bela, da Beker, da Ashbel, da Gera, da Na'aman, da Ahiram, da Rosh, da Muffim, da Huffim, da Adar.
22 Waɗannan su goma sha huɗu su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Rahila.
23 Hushim shi ne ɗan Dan.
24 'Ya'yan Naftali, maza, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum.
25 Waɗannan su bakwai, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Bilha, wadda Laban ya bai wa 'yarsa Rahila.