6 Suka kuma kora shanunsu, suka ɗauki kayayyakinsu waɗanda suka samu a ƙasar Kan'ana, suka iso Masar, Yakubu da zuriyarsa duka,
7 'ya'yansa maza da jikokinsa maza tare da shi, 'ya'yansa mata, da jikokinsa mata, ya kawo zuriyarsa dukka zuwa ƙasar Masar.
8 Waɗannan su ne sunayen 'ya'ya maza na Isra'ila, wato Yakubu, waɗanda suka iso Masar. Ra'ubainu, ɗan farin Yakubu.
9 'Ya'yan Ra'ubainu, maza kuwa, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi.
10 'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan wata Bakan'aniya.
11 'Ya'yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari.
12 'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.