9 'Ya'yan Ra'ubainu, maza kuwa, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi.
10 'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan wata Bakan'aniya.
11 'Ya'yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari.
12 'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.
13 'Ya'yan Issaka, maza, su ne Tola, da Fuwa, da Yashub, da Shimron.
14 'Ya'yan Zabaluna, maza, su ne Sered, da Elon, da Yaleyel,
15 (waɗannan su ne 'ya'yan Lai'atu, maza, waɗanda ta haifa wa Yakubu cikin Fadan-aram, da 'ya tasa kuma Dinatu, 'ya'yansa mata da maza duka, mutum talatin da uku ne).