1 Ya zama fa bayan waɗannan al'amura, aka faɗa wa Yusufu, “Ga mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki 'ya'yansa biyu maza, Manassa da Ifraimu ya tafi ya gai da mahaifinsa.
2 Sa'ad da aka ce wa Yakubu, “Ɗanka Yusufu ya zo wurinka,” sai Yakubu ya ƙoƙarta ya tashi zaune a kan gadon.
3 Yakubu ya ce wa Yusufu, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan'ana ya sa mini albarka,
4 ya ce mini, ‘Ga shi, zan sa ka hayayyafa, in riɓaɓɓanya ka, zan maishe ka ƙungiyar al'ummai, zan kuwa ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka ta zama madawwamiyar mallaka.’