1 Yakubu ya kirawo 'ya'yansa maza, ya ce, “Ku tattaru wuri ɗaya don in faɗa muku abin da zai same ku a cikin kwanaki masu zuwa.
2 “Ku taru ku ji, ya ku 'ya'yanYakubu, maza,Ku kuma kasa kunne ga Isra'ilamahaifinku.
3 “Ra'ubainu, kai ɗan farinane, ƙarfina,Ɗan balagata, isasshe kuma, mafiƙarfi duka cikin 'ya'yana.
4 Kamar ambaliyar ruwa mai fushikake,Amma ba za ka zama mafi darajaba,Domin ka hau gadon mahaifinka,Sa'an nan ka ƙazantar da shi.
5 “Saminu da Lawi 'yan'uwa ne,Suka mori takubansu cikin ta dahankali.