18 Ina zuba ido ga cetonka, yaUbangiji.
19 “Gad, 'yan fashi za su kai masa hari,Shi kuwa zai runtume su.
20 “Ashiru, ƙasarsa za ta ba da amfanimai yawa,Zai kuma yi tanadin abincin da yadace da sarki.
21 “Naftali sakakkiyar barewa ce,Mai haihuwar kyawawan 'ya'ya.
22 “Yusufu jakin jeji ne,Jakin jeji a gefen maɓuɓɓugaAholakan jeji a gefen tuddai.
23 Maharba suka tasar masa ba tausayiSuka fafare shi da kwari da baka.
24 Duk da haka bakunansu sunkakkarye.Damatsansu sun yayyageTa wurin ikon Allah Mai Girma naYakubu,Makiyayi, Dutse na Isra'ila.