1 Wannan shi ne littafin asalin Adamu. A sa'ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin siffar Allah.
2 Namiji da ta mace ya halicce su, ya sa musu albarka, ya sa musu suna, Mutum, sa'ad da aka halicce su.
3 Da Adamu ya yi shekara ɗari da talatin, ya haifi ɗa cikin kamanninsa da cikin siffarsa, ya kuwa sa masa suna Shitu.
4 Bayan da Adamu ya haifi ɗansa Shitu, ya yi shekara ɗari takwas, sa'an nan ya haifi 'ya'ya mata da maza.
5 Haka nan kuwa dukan kwanakin Adamu shekara ce ɗari tara da talatin, ya rasu.
6 Da Shitu ya yi shekara ɗari da biyar, ya haifi Enosh.
7 Bayan da Shitu ya haifi Enosh ya rayu shekara ɗari takwas da bakwai, ya haifi 'ya'ya mata da maza.